Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya bayyana cewa zai soke sunayen manyan hanyoyi, cibiyoyin gwamnati da sauran kadarorin ƙasa da aka sanya wa sunan Shugaba Bola Ahmed Tinubu idan ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Sowore ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce gwamnatinsa za ta sake duba duk wasu kadarorin gwamnati da aka raɗa wa sunayen jami’an gwamnati na yanzu.
Kalaman nasa sun biyo bayan matakin gwamnatin tarayya na sanya wa babbar hanyar Lagos–Calabar Coastal Highway sunan Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A cewar Ministan Ayyuka, David Umahi, an ɗauki matakin ne domin karrama gudunmawar Tinubu da hangen nesansa wajen aiwatar da aikin hanyar.
Sai dai Sowore ya ce idan ya zama shugaban ƙasa, zai mayar da sunayen kadarorin gwamnati zuwa yadda ya dace, yana mai cewa kadarorin ƙasa bai kamata su riƙa ɗaukar sunayen shugabannin da ke kan mulki ba.