Saturday, October 17, 2026
HomeTsaro’Yan Bindiga sun sace ’yan gudun hijirar da suka koma gidajensu a...

’Yan Bindiga sun sace ’yan gudun hijirar da suka koma gidajensu a Sokoto

Wasu ’yan gudun hijira da suka koma ƙauyukansu kwanan nan sun sake faɗa hannun ’yan bindiga bayan wani sabon hari da aka kai a ƙauyukan Gasalodi da Tungar Barke da ke Ƙaramar Hukumar Tambuwal a Jihar Sokoto.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba, inda maharan suka mamaye ƙauyukan tare da yin garkuwa da mutane da dama.

Wannan hari na zuwa ne a daidai lokacin da wasu daga cikin mazauna yankin suka fara komawa gidajensu bayan shafe lokaci suna gudun hijira sakamakon matsalar tsaro.

Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, ba a bayyana adadin mutanen da aka sace ba, kuma jami’an tsaro ba su fitar da cikakken bayani kan lamarin ba.

Al’ummar yankin na ci gaba da kira ga hukumomin tsaro da gwamnati da su ƙara ɗaukar matakan kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments