Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaShugabanci ba na masu son faranta wa kowa rai ba ne –...

Shugabanci ba na masu son faranta wa kowa rai ba ne – Kashim Shettima

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa ingantaccen shugabanci yana buƙatar jajircewa, hangen nesa da kuma yanke shawarwari masu wahala domin amfanin al’umma gaba ɗaya.

Shettima ya ce shugabanci ba aikin neman farin jini ko faranta wa kowa rai ba ne, illa dai ɗaukar matakan da suka dace ko da kuwa ba za su yi wa kowa daɗi ba a farkon lokaci.

Ya jaddada cewa shugabanni na gari sukan fifita muradun ƙasa da jin daɗin al’umma a kan neman yabo ko shahara, yana mai cewa wasu shawarwari masu wahala sukan zama wajibi domin samun ci gaba mai ɗorewa.

Kalaman nasa na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan manufofi da matakan da gwamnatin tarayya ke ɗauka kan tattalin arziki da ci gaban ƙasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments