Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu, JAMB ta gargaɗi masu neman gurbin karatu da su guji karɓar guraben karatu da aka bayar ta hanyoyin da ba su bi tsarin Central Admissions Processing System (CAPS) ba, tana mai cewa irin waɗannan guraben ba su da inganci kuma ba za a amince da su ba.
Magatakardar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana cewa gurbin karatu zai kasance sahihi ne kawai idan an sarrafa shi ta hanyar CAPS kuma and ɗalibin ya samu takardar shaidar shiga makaranta daga JAMB. Ya ce duk wata makaranta da ta ba ɗalibi gurbin karatu ba tare da bin wannan tsari ba, ta karya doka.
Ya kuma yi gargaɗin cewa duk ɗalibin da ya karɓi gurbin karatu ta “bayan fage” ba zai bayyana a cikin jerin sunayen ɗaliban da aka amince da su ba, lamarin da zai iya jefa karatunsa cikin matsala.
Oloyede ya ƙara da cewa babu wata makaranta da ke da ikon ɗaukar ɗalibai fiye da adadin da aka amince mata da shi. Ya ce duk ɗalibin da aka ƙara bayan cikar adadin da aka ware wa wani fanni, za a ɗauke shi a matsayin wanda aka ba gurbin karatu ba bisa ƙa’ida ba.
Haka kuma, ya shawarci masu neman gurbin karatu da su kare lambobin wayarsu (SIM), yana mai cewa yanzu SIM na taka muhimmiyar rawa wajen tantance bayanan ɗalibai a tsarin jarabawa da shiga manyan makarantu. Ya gargaɗe su da kada su sayi SIM da aka riga aka yi wa rajista ko kuma su amince a yi musu musayar SIM, domin hakan na iya jefa su cikin matsalar satar bayanai da zamba.