Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiMajalisar Dattawa ta amince dokar haramta wa’azi da talla a motocin haya

Majalisar Dattawa ta amince dokar haramta wa’azi da talla a motocin haya

Ƙudirin, wanda ke jiran amincewar Shugaban Ƙasa kafin ya zama doka, ya kuma ƙara tsaurara hukunci kan direbobin da ke karya dokokin hanya.

Majalisar Dattawa ta amince da gyaran dokar Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC), wanda ya tanadi hukuncin tarar ₦50,000 ga duk wanda aka kama yana yin wa’azi, talla ko kasuwanci a cikin motocin jigilar fasinja.

Sabuwar dokar ta tanadi tarar ₦50,000 ko ɗaurin watanni shida, ko kuma hukuncin duka biyun, ga direban da ya ƙi yin gwajin numfashi domin tantance ko ya sha giya ko wasu ƙwayoyi yayin binciken jami’an FRSC.

Haka kuma, an ƙara tarar tuƙi bayan shan giya ko ƙwayoyi daga naira 5,000 zuwa naira 100,000, tare da yiwuwar ɗaurin shekaru biyu idan kotu ta same shi da laifi.

Baya ga haka, tuƙin ganganci da gudun wuce kima yanzu za su jawo tarar naira 100,000, yayin da majalisar ta ce a sake duba fiye da laifukan hanya 50 domin inganta tsaron masu amfani da tituna.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments