Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa tana nazarin yiwuwar gudanar da cikakken bincike kan na’urorin fasahar zaɓenta, tare da shirya zaɓen gwaji domin tantance shirye-shiryenta kafin babban zaɓen shekarar 2027.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan (SAN), ne ya bayyana hakan a Abuja yayin da ya karɓi baƙuncin Jakadan Birtaniya a Najeriya, Dr. Richard Montgomery.
A cewarsa, matakin ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da aka samu bayan babban zaɓen 2023, inda aka buƙaci a sake duba yadda ake amfani da fasahohin zaɓe domin ƙara inganta sahihanci da amincewar jama’a.
Ya bayyana cewa gudanar da zaɓen gwaji zai bai wa INEC damar tantance yadda na’urorin BVAS da dandalin IReV ke aiki, gano duk wata matsala tun kafin ranar zaɓe, da kuma ɗaukar matakan gyara.
Shugaban INEC ya ƙara da cewa duk da cewa ba a ware kuɗaɗen wannan shiri a kasafin kuɗin farko na hukumar ba, za a nemo hanyoyin aiwatar da shi saboda muhimmancinsa ga inganta tsarin zaɓe.
Hukumar ta kuma bayyana aniyarta ta ƙarfafa tsarin tsaron yanar gizo da kuma ci gaba da haɗin gwiwa da ƙasashen duniya, musamman Birtaniya, wajen bunƙasa fasahar gudanar da zaɓe.
A nasa ɓangaren, Jakadan Birtaniya, Dr. Richard Montgomery, ya yaba da ƙoƙarin INEC na inganta tsarin zaɓe, yana mai cewa ƙasarsa za ta ci gaba da mara wa Najeriya baya wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya.
Wannan na zuwa ne bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da ingancin jadawalin zaɓen 2027 da INEC ta fitar, tare da jaddada cewa hukumar na da cikakken ikon tsara ranakun gudanar da zaɓe bisa tanadin dokar zaɓe ta 2026.