Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiEFCC ta nemi ƙarin haɗin gwiwa domin dakile ɗaukar nauyin ta’addanci da...

EFCC ta nemi ƙarin haɗin gwiwa domin dakile ɗaukar nauyin ta’addanci da kare ƙungiyoyin fararen hula

Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Ta’annati ta EFCC ta yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatoci, hukumomi masu sa ido da ƙungiyoyin fararen hula CSOs a faɗin Afirka domin dakile hanyoyin da ake bi wajen ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci, tare da kare ƙungiyoyin agaji da na fararen hula daga tsauraran dokoki da ka iya hana su gudanar da ayyukansu.

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana hakan yayin taron Africa High-Level Civil Society Anti-Money Laundering and Combating the Financing of Terrorism Conference da aka gudanar a Abuja. Ya ce ya zama wajibi a samar da daidaito tsakanin yaƙi da safarar kuɗaɗe da ɗaukar nauyin ta’addanci, da kuma kare ayyukan halastattun ƙungiyoyin fararen hula.

Ya bayyana cewa wasu ƙungiyoyin ta’addanci na amfani da hanyoyin kuɗi da kuma wasu ƙungiyoyin bogi wajen samun kuɗaɗen gudanar da ayyukansu, lamarin da ke buƙatar ƙarin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, masu tsara dokoki da ƙungiyoyin fararen hula domin gano da dakile irin waɗannan hanyoyi.

Olukoyede ya kuma jaddada cewa yaƙi da ɗaukar nauyin ta’addanci bai kamata ya haifar da takura ga ƙungiyoyin fararen hula masu gudanar da ayyukan jin ƙai ba. Ya ce ya zama dole a aiwatar da ƙa’idojin Financial Action Task Force (FATF) yadda ya kamata, ba tare da tauye haƙƙin ƙungiyoyin da ke gudanar da halastattun ayyuka ba.

Masu halartar taron sun buƙaci ƙasashen Afirka su ƙara musayar bayanan sirri, inganta dokokin yaƙi da safarar kuɗaɗe da ɗaukar nauyin ta’addanci, tare da gina amincewa tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin fararen hula domin tabbatar da ingantaccen tsaro da kare sararin gudanar da ayyukan jin ƙai a nahiyar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments