Dakarun Bataliya ta 195 tare da haɗin gwiwar (CJTF) sun kama wani mutum da ake zargi da yi wa ƙungiyar ta’addanci ta ISWAP leƙen asiri a ƙaramar hukumar Mafa da ke Jihar Borno.
A cewar mai sanya ido kan harkokin tsaro a yankin Sahel, Zagazola Makama, an kama wanda ake zargin ne da misalin ƙarfe 11:30 na dare a ranar 14 ga watan Yuli yayin wani samame da aka gudanar bisa sahihan bayanan sirri a yankin Dusuman.
Rahotanni sun nuna cewa binciken farko ya gano mutumin na da alaƙa da wasu mambobin ƙungiyar ISWAP, kuma ana zargin yana isar musu da muhimman bayanai da ka iya taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu.
A halin yanzu, jami’an tsaro sun tsare wanda ake zargin domin ci gaba da gudanar da bincike tare da gano cikakken matsayinsa da kuma ko akwai wasu da suke haɗa kai da shi.
Wannan nasara na zuwa ne yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da ƙara matsin lamba kan ƙungiyoyin ta’addanci da masu ba su bayanan sirri a yankin Arewa maso Gabas.