Hukumar Kula da Asusun Fansho ta Ƙasa (PenCom) ta sanar da cewa darajar kadarorin fansho a Najeriya ta ƙaru da kashi 51 cikin ɗari cikin shekaru biyu da suka gabata, lamarin da ke nuna ci gaba a tsarin gudanar da asusun fansho na ƙasar.
A cewar hukumar, darajar kadarorin ta tashi daga Naira tiriliyan 20.79 zuwa Naira tiriliyan 31.48, yayin da adadin mambobin da ke cikin tsarin(CPS) ya ƙaru da kusan mutum miliyan ɗaya, inda ya kai miliyan 11.32.
Babbar Daraktar PenCom, Omolola Oloworaran, ce ta bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a ranar Litinin, inda ta ce ci gaban ya samo asali ne daga bunƙasar tsarin fansho da kuma ƙarin masu shiga shirin.
Ta bayyana cewa hukumar za ta ci gaba da aiwatar da manufofin da za su ƙara inganta tsarin fansho, kare haƙƙin masu ajiya da kuma tabbatar da gudanar da asusun cikin gaskiya da inganci.
PenCom ta jaddada cewa ƙarfafa tsarin fansho na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da walwalar ma’aikata bayan sun yi ritaya, tare da taimakawa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa ta hanyar zuba jari cikin tsari.