Sunday, October 18, 2026
HomeTsaroJama'ar gari sun yi kukan kura, an kama ɗan bindiga a Kano

Jama’ar gari sun yi kukan kura, an kama ɗan bindiga a Kano

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da kasancewa ɗaya daga cikin ɓarayin daji masu aikata laifuka a ƙaramar hukumar Bichi.

A cewar rundunar, an kama wanda ake zargin ne a wani samame da jami’an tsaro suka gudanar, inda aka kuma ƙwato harsasai 109 da wasu kayayyakin da ake zargin an shirya kai wa ’yan bindiga.

Mai magana da yawun rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, yana mai cewa kamen na daga cikin matakan da rundunar ke ɗauka na daƙile ayyukan masu laifi a jihar.

Ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna akwai alaƙa tsakanin wanda ake zargin da wasu masu aikata laifukan ta’addanci, kuma jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike domin gano sauran waɗanda ke da hannu a lamarin.

Rundunar ta sake tabbatar da aniyarta ta ci gaba da yaƙi da ‘yan bindiga da sauran masu aikata manyan laifuka, tare da kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanan da za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments