Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiNiMet ta yi hasashen hadari da tsawa na kwana uku a wasu...

NiMet ta yi hasashen hadari da tsawa na kwana uku a wasu sassa na kasar

Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya NiMet ta yi hasashen cewa za a samu yanayi mai gajimare tare da ruwan sama da tsawa a sassa daban-daban na ƙasar daga ranar Laraba har zuwa Juma’a.

Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya NiMet ta yi hasashen cewa za a samu yanayi mai gajimare tare da ruwan sama da tsawa a sassa daban-daban na ƙasar daga ranar Laraba har zuwa Juma’a.

NiMet ta ce jihohin Arewa, Arewa ta Tsakiya da Kudancin ƙasar za su fuskanci ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi tare da tsawa a lokuta daban-daban na yini, yayin da wasu yankuna za su fara da gajimare kafin ruwan sama ya biyo baya.

Hukumar ta kuma yi gargaɗin cewa iska mai ƙarfi na iya gabatar da ruwan sama a wuraren da ake sa ran tsawa, tare da buƙatar jama’a su ɗaure abubuwan da iska za ta iya ɗauka domin kauce wa haɗurra.

NiMet ta shawarci direbobi da su guji tuki lokacin da ake ruwan sama mai ƙarfi, sannan a cire kayan lantarki daga soket yayin tsawa. Ta kuma gargaɗi mutane da su guji fakewa a ƙarƙashin manyan bishiyoyi saboda haɗarin faɗuwar rassan bishiya.

Hukumar ta buƙaci mazauna ƙasar su ci gaba da bibiyar sabbin hasashen yanayi daga NiMet, yayin da ta shawarci kamfanonin jiragen sama su riƙa samun rahotannin yanayi na filayen jiragen sama domin sauƙaƙa shirye-shiryen zirga-zirgarsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments