Ɗan takarar shugaban Najeriya na jam’iyyar AAC a zaɓen 2027, Omoyele Sowore, ya bayyana tsarin manufofin ilimi na jam’iyyarsa, inda ya yi alƙawarin samar da ilimi kyauta daga matakin firamare har zuwa jami’a idan aka zaɓe shi.
A cikin manufofin da ya wallafa, Sowore ya ce gwamnatinsa za ta ɗauki nauyin kuɗin jarabawar gwamnati kamar WAEC da NECO, domin tabbatar da cewa babu ɗalibin da talauci zai hana ci gaba da karatu.
Ya kuma yi alƙawarin inganta tsarin ilimi ta hanyar samar da dakunan karatu na zamani, ƙarin albashi da walwala ga malamai, tallafin karatu ga ɗalibai, da kuma sake fasalin tsarin karatu zuwa shekaru biyar na firamare, biyar na sakandare da shekaru huɗu na jami’a.
Bugu da ƙari, Sowore ya ce zai kafa kwalejin karatun shekaru biyu a kowace ƙaramar hukuma, ya mayar da kwalejojin kimiyya da fasaha zuwa jami’o’i, tare da kare haƙƙin ƙungiyoyin ɗalibai da ƙarfafa bincike a fannoni kamar lafiya, makamashi da fasahar AI.
Ɗan takarar ya bayyana cewa manufofin nasa sun fi mayar da hankali ne kan tabbatar da cewa kowane yaro ya samu damar ilimi ba tare da la’akari da matsayinsa na tattalin arziki ba, yana mai cewa wannan ba alkawarin siyasa kawai ba ne, illa wata hanya ta gina Najeriya mai ingantaccen ilimi.