Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiFursunoni 61 sun sauke Alƙur’ani a gidan gyaran hali na Kurmawa da...

Fursunoni 61 sun sauke Alƙur’ani a gidan gyaran hali na Kurmawa da ke Kano

Fursunoni 61 da ke tsare a Gidan Gyaran Hali na Kurmawa a Jihar Kano sun yi saukar Alƙur’ani bayan kammala karatunsu a wani shiri na gyaran hali ta hanyar ilimi da koyarwar addini.

Masu saukar sun haɗa da maza 55 da mata shida.

Hukumar Gyaran Hali ta bayyana cewa da dama daga cikinsu ba su da cikakken ilimin karatun Alƙur’ani kafin shigarsu gidan gyaran hali, amma sun samu damar koyo da kuma haddace karatun yayin zamansu a cibiyar.

Kwanturolan Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano, Ahmed Yusuf Lakpene, ya ce wannan nasara ta nuna irin tasirin shirye-shiryen gyaran hali da ake gudanarwa, musamman ta fuskar ilimi da tarbiyyar addini, domin sauya rayuwar masu zaman gidan gyaran hali.

Shi ma Shugaban Gidan Gyaran Hali na Kurmawa, DCC Ibrahim Isah Rambo, ya yabawa malamai da sauran masu ruwa da tsaki bisa haɗin kai da suka bayar, wanda ya taimaka wajen samun wannan gagarumar nasara.

A wajen bikin, Hakimin Dan Ruwatan Kano, Alhaji Ibrahim Ado Bayero, ya miƙa takardun shaidar kammala saukar Alƙur’ani ga fursunonin 61, tare da ƙarfafa musu gwiwa su ci gaba da riko da koyarwar Alƙur’ani bayan kammala wa’adin zamansu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments