Wasu masu garkuwa da mutane sun kai hari kan tawagar da ke ɗauke da gawar tsohon Mataimakin Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC), Augustine O. Ikwue, yayin da ake kan hanyar kai gawarsa garinsu na Otukpo da ke jihar Benue domin yi masa jana’iza.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:00 na yammacin ranar Alhamis a hanyar Ochadamu zuwa Ejule, cikin ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi.
Maharan sun sace gawar marigayin tare da wasu daga cikin mutanen da ke cikin tawagar, lamarin da ya tayar da hankalin iyalansa da jami’an tsaro.
Rahotanni sun nuna cewa masu garkuwar sun tuntubi iyalan marigayin tare da neman kuɗin fansa har naira miliyan 450 domin sakin mutanen da suke tsare da su.
Kwamandan FRSC na jihar Kogi, Lawal Fagge, ya tabbatar da cewa mutum tara ne aka yi garkuwa da su, ciki har da jami’an FRSC biyu.
Sai dai Fagge ya ce daga baya jami’an tsaro sun gano gawar marigayin a yankin Ejule, inda aka miƙa ta ga iyalansa domin gudanar da jana’izarsa.
Ya kuma bayyana cewa masu garkuwar sun yi amfani da wayar marigayin wajen kiran matarsa domin sanar da ita buƙatar kuɗin fansa.
A halin yanzu, jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji, ’yan sanda, mafarauta da masu sintiri sun bazama yankin domin ceto sauran mutanen da aka yi garkuwa da su tare da cafke waɗanda suka aikata wannan hari.