Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC ta ƙara wa’adin da ta bai wa jam’iyyun siyasa na miƙa sunayen ’yan takararsu domin zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya na 2027 da ƙarin kwanaki uku.
A wata sanarwa da Kwamishinan INEC kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Ilimantar da Masu Zaɓe, Mohammed Kudu Haruna, ya sanya wa hannu, hukumar ta ce sabon wa’adin zai ƙare da tsakar daren ranar Talata, 14 ga Yuli, 2026, maimakon ranar Asabar, 11 ga Yuli.
INEC ta bayyana cewa ta ɗauki matakin ne bayan roƙon da Majalisar Ba da Shawara ta Jam’iyyun Siyasa (IPAC) ta gabatar a madadin jam’iyyun da ba su samu damar loda sunaye da bayanan ‘yan takararsu cikin wa’adin da aka gindaya ba.
Hukumar ta ce ƙarin wa’adin ya nuna aniyarta ta tabbatar da cewa kowane ɓangare ya samu damar shiga tsarin zaɓe cikin adalci tare da bin tanadin doka.
INEC ta kuma buƙaci dukkan jam’iyyun siyasa su yi amfani da wannan ƙarin lokaci wajen kammala loda sunaye da sauran bayanan ‘yan takararsu kafin sabon wa’adin ya cika.