Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa ya ƙi biyan kuɗin fansa na Naira miliyan 300 bayan masu garkuwa da mutane suka sace ‘yan uwansa a shekarar 2019, yana mai cewa ya fi son su kashe su maimakon ya ba masu laifin kuɗi.
Dauda Lawal ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin taron Arise News da Thisday da aka gudanar a Abuja.
Gwamnan ya kare matsayinsa na kin biyan kuɗin fansa tare da jaddada cewa biyan kuɗi ga masu garkuwa da mutane yana ƙara musu ƙwarin gwiwar ci gaba da aikata laifin.
Ya ce:
“An sace ‘yan uwana a shekarar 2019, kuma a lokacin waɗannan masu laifi suna neman kusan Naira miliyan 300. Sai na ce, ba zan biya ko sisi ba. Idan kuna so, ku kashe su.”
Gwamnan ya ce daga bisani ‘yan uwansa sun samu ‘yanci bayan sun shafe watanni uku a hannun masu garkuwar, ba tare da an biya ko kwabo ɗaya na kuɗin fansa ba.
A cewarsa, ci gaba da biyan kuɗin fansa yana ƙarfafa ƙungiyoyin masu laifi tare da ƙara musu sha’awar ci gaba da sace mutane domin neman kuɗi.