Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTinubu ya gana da shugabannin tsaro kan matsalar rashin tsaro

Tinubu ya gana da shugabannin tsaro kan matsalar rashin tsaro

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci wani muhimmin taron tsaro a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Alhamis, inda ya gana da hafsoshin rundunonin soji, shugabannin hukumomin leƙen asiri da sauran manyan jami'an tsaro domin nazarin halin tsaron ƙasar.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci wani muhimmin taron tsaro a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Alhamis, inda ya gana da hafsoshin rundunonin soji, shugabannin hukumomin leƙen asiri da sauran manyan jami’an tsaro domin nazarin halin tsaron ƙasar.

An gudanar da taron na fiye da sa’o’i biyu. Ya samu halartar Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu; Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa; Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Olufemi Oluyede; Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Isa; Babban Hafsan Leƙen Asirin Soji, Laftanar Janar Emmanuel Undiandeye; Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Olatunde Disu; Darakta Janar na Hukumar DSS, Adeola Ajayi; Darakta Janar na Hukumar NIA, Mohammed Mohammed; da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaron Cikin Gida, Manjo Janar Adeyinka Famadewa (mai ritaya), tare da sauran manyan jami’an tsaro..

Majiyoyin da suka san abin da aka tattauna sun ce taron ya mayar da hankali ne kan duba halin da tsaro ke ciki a faɗin ƙasar da kuma ayyukan soji da ake gudanarwa a sassa daban-daban.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments