Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroFashewar bam ya hallaka jami’an soji uku a Neja

Fashewar bam ya hallaka jami’an soji uku a Neja

Wani Kyaftin da sojoji biyu na rundunar sojin Najeriya sun rasa rayukansu bayan wata motar sintiri ta taka bam da aka birne a kan hanya a ƙauyen Maciyan-Kyada da ke gundumar Babanna, ƙaramar hukumar Borgu a jihar Neja.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar Talata yayin da dakarun ke gudanar da sintirin tabbatar da tsaro.

Wata majiya ta tsaro ta bayyana cewa sojojin sun bar Babanna da misalin ƙarfe 10:00 na safe kafin ɗaya daga cikin motocinsu ta taka bam ɗin da ake zargin wasu masu ɗauke da makamai sun dasa a hanya.

Majiyar ta ƙara da cewa fashewar ta yi sanadin mutuwar jami’ai uku, ciki har da wani Kyaftin, yayin da wasu sojoji biyu suka samu munanan raunuka kuma aka garzaya da su domin samun kulawar likitoci.

Wani mazaunin yankin da ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce ɗaya daga cikin waɗanda suka mutu ana kiransa Yusuf Kabir.

Ya bayyana cewa harin ya ƙara jefa al’ummar yankin cikin fargaba saboda matsalolin tsaro da hare-haren masu ɗauke da makamai da kuma garkuwa da mutane da ake ci gaba da fuskanta.

Ya zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, rundunar sojin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba, yayin da ake ci gaba da tattara ƙarin bayanai.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments