Mazauna aƙalla ƙauyuka 30 da ke gundumar Danchadi a Ƙaramar Hukumar Bodinga ta jihar Sokoto sun tsere daga gidajensu sakamakon hare-haren da ’yan bindiga ke ci gaba da kaiwa yankin.
Hakan na ƙunshe ne cikin wani rahoto da Hakimin Danchadi, Alhaji Lirwanu Mafaran, Kuwarun Sarkin Musulmi, ya sanya wa hannu tare da aikewa shugaban Ƙaramar Hukumar Bodinga da hukumomin tsaro.
Rahoton ya bayyana cewa hare-haren da aka kai tsakanin Laraba, 1 ga Yuli da Alhamis, 2 ga Yuli, 2026 sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutum shida, tare da tilasta daruruwan mazauna ƙauyukan tserewa daga gidajensu.
Haka kuma, ’yan bindigan sun sace fiye da dabbobi 1,000 da suka haɗa da shanu da rakuma, musamman a ƙauyukan Kyaluje da Dibarke.
An kuma aika kwafin rahoton ga jami’an hukumar ’yan sanda DPO, Hukumar NSCDC da DSS domin ɗaukar matakan da suka dace.
Wani babban basarake a gundumar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da sahihancin rahoton, yana mai cewa shi da kansa ya kai kwafinsa ga hukumomin tsaro da ke aiki a yankin.
Daga cikin ƙauyukan da hare-haren suka shafa akwai Gidan Gadanga, Gidan Dan Bube, Dutsin Mai Gunya, Batsauje, Sire Modi, Gwantsi, Kore Maiganga, Bangi Rafi, Bangi Dutsin, Yabawa, Lageji, Bille, Gonin Gari, Wumumu, Chohi, Saran Malan, Wure Yal’dde, Gidan Hodi, Dabugi, Rukusawa, Tunga, Lakes, Maikataru, Dutsin Toka, Karaje, Kwantsi Buga, Yan Gidaje, Runbuki, Kwantsi Tunga da Lau Gari.