A yau ake bikin Ranar Sumbata ta Duniya wato “International Kissing Day”, ranar da ake amfani da ita wajen nuna muhimmancin sumbata a matsayin wata hanya ta nuna ƙauna, girmamawa da kusanci tsakanin mutane.
Masana sun bayyana cewa ba mutane kaɗai ke yin sumbata ba. Wasu dabbobi ma na yin irin wannan ɗabi’a, amma ba saboda sha’awa ko soyayya ba. A cewarsu, dabbobin na yin hakan ne domin isar da saƙo, ƙarfafa alaƙa a tsakaninsu, nuna amincewa, ko kuma kula da junansu.
Masana sun ce wannan na nuna cewa sumbata na da ma’anoni daban-daban a halittu, kuma ba koyaushe take nufin soyayya ko sha’awa ba.