Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiKwankwaso ya jajanta wa Sanata Baba Tela kan rasuwar ‘ya’yansa biyu

Kwankwaso ya jajanta wa Sanata Baba Tela kan rasuwar ‘ya’yansa biyu

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya miƙa saƙon ta’aziyya ga tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Baba Tela, bisa rasuwar ‘ya’yansa biyu, Mustapha da Ummi, a wani hatsarin mota.

A cikin wata sanarwa, Kwankwaso ya bayyana cewa rasuwar ta jefa iyalan mamatan cikin babban baƙin ciki, tare da girgiza al’ummar Masarautar Katagum da ma jihar Bauchi baki ɗaya.

Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga gwamnatin jihar Bauchi da ɗaukacin al’ummar jihar, yana addu’ar Allah ya jiƙan Mustapha da Ummi, Ya gafarta musu kura-kuransu, sannan Ya bai wa iyalansu da ’yan uwansu haƙurin jure wannan babban rashi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments