Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTsananin yunwa a Arewa abin tayar da hankali ne – Peter Obi

Tsananin yunwa a Arewa abin tayar da hankali ne – Peter Obi

Ɗan takarar shugaban Najeriya na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Peter Obi, ya bayyana damuwarsa kan yadda matsalar yunwa ke ƙara ta’azzara a yankin Arewacin Najeriya.

Obi ya ce halin da miliyoyin mutane ke ciki na nuna buƙatar gaggawar ɗaukar matakan da za su rage raɗaɗin matsalar tare da inganta wadatar abinci da rayuwar al’umma.

Kalaman nasa sun biyo bayan wani sabon rahoto da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar, wanda ya nuna cewa sama da mutum miliyan 17 a jihohi tara na Arewacin Najeriya na fuskantar matsananciyar yunwa.

Rahoton, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, ya bayyana cewa rikice-rikice, sauyin yanayi da matsin tattalin arziki na daga cikin manyan abubuwan da suka haddasa ƙaruwar rashin wadatar abinci a yankin.

Peter Obi ya buƙaci gwamnati da masu ruwa da tsaki su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen samar da mafita mai ɗorewa domin rage yunwa da inganta rayuwar al’ummar da abin ya shafa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments