Wasu daga cikin iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na Najeriya sun bayyana cewa gwamnati da hukumomin tsaro sun yi watsi da ƙoƙarin ceto ‘yan’uwansu, duk da alkawuran da aka yi musu tun farko.
Wani bincike da jaridar Punch ta gudanar ya nuna cewa iyalan da dama sun ce a farkon lamarin jami’an gwamnati da na tsaro sun riƙa tuntubar su tare da ba su tabbacin cewa ana aiki domin kuɓutar da waɗanda aka sace.
Sai dai, a cewarsu, bayan shafe watanni ba tare da wani ci gaba ba, sadarwa tsakanin su da hukumomin ta ragu, lamarin da ya ƙara musu damuwa da rashin tabbas kan makomar ‘yan’uwansu.
Binciken ya kuma nuna cewa wasu daga cikin iyalan sun koka da rashin samun bayanai kan inda aka kwana da matakan da ake ɗauka, duk da ci gaba da jiran cikar alkawuran da aka yi musu.
Da aka nemi jin ta bakin hukumomin da abin ya shafa, wasu sun bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da ƙoƙarin ceto mutanen da aka sace, yayin da wasu hukumomin ba su bayar da wata amsa ba.