Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Kano na shirin samar da mayankar dabbobi na zamani

Gwamnatin Kano na shirin samar da mayankar dabbobi na zamani

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana shirinta na yin aiki kafada da kafada da Gwamnatin Tarayya domin inganta harkokin kiwon dabbobi, ta hanyar aiwatar da manyan ayyukan raya fannin da za su bunƙasa tattalin arzikin jihar.

Mataimakin Gwamnan Kano, Murtala Sule Garo, ne ya bayyana hakan yayin da ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen karɓar baƙuncin Ministan Bunƙasa Kiwon Dabbobi, Idi Mukhtar Maiha, a Kano.

Ya ce gwamnatin jihar ta kuduri aniyar kafa mayankan dabbobi na zamani da suka dace da ƙa’idojin lafiya da kasuwanci, tare da ƙarfafa sassan kiwon dabbobi, kaji da kifaye domin samar da ƙarin abinci da guraben aikin yi ga al’umma.

Haka kuma, gwamnatin ta bayyana cewa za ta mayar da hankali wajen bunƙasa sarrafa madarar shanu da kuma farfaɗo da masana’antun sarrafa fata, domin ƙara wa kayayyakin da ake samarwa a jihar ƙima da kuma bunƙasa fitar da su zuwa kasuwannin cikin gida da na ƙasashen waje.

A nasa jawabin, Ministan Bunƙasa Kiwon Dabbobi, Idi Mukhtar Maiha, ya yabawa Gwamnatin Jihar Kano bisa ƙirƙirar Ma’aikatar Bunƙasa Kiwon Dabbobi, yana mai cewa hakan ya nuna aniyar gwamnati na bai wa fannin kulawar da ta dace.

Ministan ya kuma jinjinawa ƙoƙarin gwamnatin jihar na farfaɗo da masana’antun fata, tare da matakan da take ɗauka wajen ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin manoma da makiyaya, yana mai bayyana cewa irin wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki da tabbatar da wadatar abinci a ƙasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments