Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnan Kebbi ya naɗa mai ba shi shawara kan harkokin makabartu

Gwamnan Kebbi ya naɗa mai ba shi shawara kan harkokin makabartu

Gwamnan Jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, ya amince da naɗin Ahmed Tijjani Musa Jega a matsayin Mai Ba Shi Shawara na Musamman kan harkokin makabartu a jihar.

Sanarwar naɗin ta fito ne ta hannun Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi, Yakubu B. Tafida, inda ya bayyana cewa naɗin ya fara aiki nan take.

A cewar sanarwar, sabon mai ba da shawarar zai rika bai wa gwamnatin jihar shawarwari kan yadda za a inganta gudanarwa, tsari da kula da makabartu a faɗin Jihar.

Naɗin na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka na cike muƙamai da nufin inganta ayyukan gwamnati da samar da ingantaccen tsarin gudanarwa a fannoni daban-daban.

Ana sa ran Ahmed Tijjani Musa Jega zai yi aiki tare da hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da kyakkyawan tsari da gudanar da harkokin makabartu yadda ya kamata.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments