Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun hallaka wani yaro mai shekara 10 tare da sace aƙalla mutane 43 a hare-haren da suka kai ƙauyukan Takatsaba da Tarah da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.
Rahotanni sun ce maharan ɗauke da manyan makamai sun kai farmakin ne a daren Laraba, inda suka riƙa harbe-harbe kafin su kutsa cikin gidaje suna sace mazauna ƙauyukan.
Wata majiya daga yankin ta bayyana cewa yaron da aka kashe ɗa ne ga Abdullahi Ado.
Ta kuma ce daga cikin waɗanda aka sace akwai mata, yara da matar babban limamin ƙauyen.
A cewar majiyar, mutum tara an sace su daga gidan Mamman Dogo, biyar daga gidan Abdullahi Ado, biyu daga gidan Mai Unguwa, yara marayu biyu daga gidan marigayi Malam Sani, mutum takwas daga gidan Malam Abubakar, da kuma mutum biyar daga gidan Amadu Siro.
An kuma bayyana cewa wasu mazauna ƙauyen har yanzu ba a san inda suke ba, bayan da suka tsere zuwa cikin daji domin tsira da rayukansu yayin harin.
Mazauna yankin sun koka kan cewa ba a samu isowar jami’an tsaro cikin lokaci ba.
Sun ce duk da ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi, maharan sun shigo ta wata hanya daban, suka aiwatar da harin kafin su tsere.
Rahotanni sun nuna cewa wannan ba shi ne karo na farko da aka kai hari a yankin ba, domin an ce mako guda da ya gabata jami’an tsaro sun samu nasarar dakile wani makamancin farmaki a ƙauyen.