Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da ceto wasu ƙananan yara tare da kama wani matashi da ake zargi da hannu wajen safarar yara zuwa ƙasashen Larabawa da sunan samar musu da aikin yi.
Mataimakin Kwamandan Hukumar Hisbah, Dr. Mujaheed Aminudeen, ya tabbatar da hakan ga DCL Hausa, inda ya ce an dakile yunkurin ne kafin a fitar da yaran daga ƙasar.
Waɗanda abin ya shafa sun haɗa da Bala Haruna, mai shekara 25 daga Kazaure a Jihar Jigawa, wanda ake zargi da kasancewa dillalin safarar yara.
Sauran sun haɗa da Fatima Sufiyanu, mai shekara 23 daga Daura a Jihar Katsina, da kuma A’isha Haruna, mai shekara 11 daga Kazaure a Jigawa.
Rahotanni sun nuna cewa an kama su ne a lokacin da ake shirin tafiya da yaran zuwa ƙasashen Larabawa, lamarin da Hisbah ta ce na iya jefa su cikin haɗarin cin zarafi, tauye haƙƙinsu na ilimi, da kuma lalata tarbiyyarsu.
Bayan kammala binciken farko, Hukumar Hisbah ta miƙa waɗanda ake zargin ga Hukumar Hana Safarar Mutane ta Kasa (NAPTIP) domin ci gaba da bincike kan zargin fataucin mutane da safarar yara.
Hukumar ta kuma yi kira ga iyaye da masu kula da yara da su guji amincewa da tura ƙananan yara zuwa ƙasashen waje da sunan neman aiki, tana mai gargadin cewa irin waɗannan matakai na iya jefa rayuwar yaran cikin mummunan haɗari.