Sunday, October 18, 2026
HomeSiyasaIdan na zama shugaban Najeriya zan soke JAMB da NYSC – Sowore

Idan na zama shugaban Najeriya zan soke JAMB da NYSC – Sowore

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC kuma ɗan fafutukar kare haƙƙin jama’a, Omoyele Sowore, ya ce zai soke hukumomin JAMB da NYSC idan aka zaɓe shi a matsayin Shugaban Najeriya.

Sowore ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, inda ya ce hukumomin biyu sun tsufa kuma lokaci ya yi da za a maye gurbinsu da tsarin da zai fi cancanta, ƙwarewa da samar da aiki.

Ya ce bai dace a ci gaba da barin JAMB ta tantance ɗaliban da jami’o’i za su ɗauka ba, yana mai zargin cewa hukumar ta zama nauyi ga al’umma da kuma asarar kuɗin jama’a.

Haka kuma, ya ce idan aka ba shi dama ya jagoranci ƙasar, zai soke shirin hidimar ƙasa na NYSC tare da maye gurbinsa da wani tsari na koyon sana’o’i da horar da matasa kan dogaro da kai bayan kammala karatun jami’a.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments