Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana damuwa kan halin da dubban mutane ke ciki a Venezuela, tana mai cewa suna buƙatar abinci, ruwan sha da matsuguni cikin gaggawa bayan girgizar ƙasa data afku a ƙasar.
Hukumar kula da ’yan gudun hijira ta MDD ta ce ƙarancin abinci ya tsananta, ayyukan yau da kullum sun tsaya cik, yayin da hanyoyin sadarwa suka lalace musamman a birnin La Guaira, wanda ya fi fuskantar mummunar barna.
A wani mataki na tallafa wa ayyukan ceto, rundunar sojin Amurka ta sake buɗe tashar jirgin ruwa domin sauƙaƙa isar da kayan agaji.
Rahotanni sun nuna cewa adadin waɗanda suka mutu ya kai kusan mutum 2,000, yayin da har yanzu ake neman dubban mutanen da ba a san inda suke ba.