Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiGwamnatin Tarayya ta umarci masu sayar da fetur da su rage farashi

Gwamnatin Tarayya ta umarci masu sayar da fetur da su rage farashi

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta umarci masu kasuwancin man fetur da su rage farashin litar fetur, bayan da aka samu saukar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.

Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, ne ya ba da umarnin yayin wani taron hukumomin da ke kula da harkokin man fetur da aka gudanar an Abuja.

A cewarsa, bayan sassautawar rikicin da ya dabaibaye Iran da Amurka, farashin ɗanyen mai ya ragu a kasuwannin duniya, don haka ya dace farashin fetur a cikin gida ma ya sauka.

Ministan ya kuma nuna rashin jin daɗinsa kan yadda wasu masu kasuwancin fetur suka ƙi rage farashin duk da sauyin da aka samu, yana mai jaddada cewa tsarin kasuwa mai ‘yanci bai kamata ya zama hanyar cin moriyar jama’a ba.

Ya ce dokar Petroleum Industry Act (PIA) ta 2021 ta bai wa hukumomin da ke kula da harkokin man fetur ikon tabbatar da cewa kasuwar ba ta cutar da masu amfani.

Lokpobiri ya kuma tunatar da masu sayar da fetur cewa duk wanda ya biya kuɗin lita 10 dole ne ya samu cikakkiyar lita 10 ba tare da an yi masa ragi ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments