Wasu ’yan Najeriya mazauna ƙasar Afirka ta Kudu sun nemi mafaka a ofishin jakadancin Najeriya da ke Pretoria sakamakon fargabar zanga-zangar nuna ƙyamar baƙi da aka shirya gudanarwa a wasu sassan ƙasar.
Rahotanni sun nuna cewa mutane da dama sun taru a harabar ofishin jakadancin domin neman kariya, bayan yaɗuwar kiraye-kirayen gudanar da zanga-zangar da ake zargin za ta iya janyo hare-hare kan baƙi, musamman ’yan ƙasashen Afirka.
A cikin wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, an ga ’yan Najeriya da iyalansu suna isa ofishin jakadancin tare da neman taimako saboda fargabar abin da ka iya faruwa.
Jakadancin Najeriya ya buƙaci ’yan ƙasar da su kwantar da hankalinsu tare da bin umarnin hukumomin tsaro na Afirka ta Kudu. Haka kuma ya ce yana ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki tare da ɗaukar matakan kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya da ke zaune a ƙasar.