Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiRikicin yan bindiga ya raba kusan mutane 800,000 da muhallansu a Arewa...

Rikicin yan bindiga ya raba kusan mutane 800,000 da muhallansu a Arewa maso Yamma

Wani sabon rahoton Hukumar Kula da Ƙaurar Baƙi ta Majalisar Ɗinkin Duniya (IOM) ya nuna cewa rikicin tsaro ya tilasta wa kusan mutane 794,000 barin muhallansu a jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Rahoton ya bayyana cewa wani hari da ƴan bindiga suka kai ƙauyen Gamon Gidan Bita da ke ƙaramar hukumar Gummi a Jihar Zamfara ya raba mutane 484 da gidajensu, ciki har da yara 271.

Bayan harin, mazauna ƙauyen sun tsere zuwa yankunan da ke makwabtaka domin neman mafaka, yayin da hukumomi suka fara tantance irin asarar da aka yi da kuma shirye-shiryen kai agajin gaggawa.

IOM ta ce daga watan Disambar 2025 zuwa Yunin 2026, sama da mutane 143,000 sun rasa matsugunansu sakamakon hare-hare a yankin, lamarin da ya sa jimillar masu gudun hijira a Arewa maso Yamma ta kusan kai 800,000.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments