Babbar Kotun Jihar Ekiti ta yanke wa Ibrahim Abubakar da Abdullahi Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same su da laifin sace wata ma’aikaciyar Hukumar Yi Wa Ƙasa Hidima (NYSC).
Mai Shari’a Lekan Ogunmoye ne ya yanke hukuncin a zamansa da ke Ado-Ekiti, bayan kotun ta tabbatar da cewa masu laifin sun aikata satar Omoboade Adesina, wadda ke yi wa ƙasa hidima a jihar, a ranar 22 ga Afrilu, 2022.
Kotun ta kuma wanke mutum na uku, Usman Abubakar, bayan ta ce masu gabatar da ƙara sun kasa gabatar da hujjojin da za su tabbatar da cewa yana da hannu a aikata laifin.
Rahotanni sun nuna cewa binciken da Hukumar Tsaro ta DSS ta gudanar ne ya kai ga cafke waɗanda aka gurfanar tare da tabbatar da shari’ar.