Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Katsina ta ki yin tsokaci kan cafke waɗanda ake zargin ’yan...

Gwamnatin Katsina ta ki yin tsokaci kan cafke waɗanda ake zargin ’yan bindiga ne a filin jirgin sama

Gwamnatin Jihar Katsina ta ce ba za ta yi tsokaci ba kan rahotannin da ke cewa an cafke wasu da ake zargin shugabannin ƴan bindiga ne bayan dawowarsu daga aikin Hajji ta Filin Jirgin Sama na Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina.

Gwamnatin Jihar Katsina ta ce ba za ta yi tsokaci ba kan rahotannin da ke cewa an cafke wasu da ake zargin shugabannin ƴan bindiga ne bayan dawowarsu daga aikin Hajji ta Filin Jirgin Sama na Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Nasiru Mu’azu Danmusa, ya bayyana cewa batun yana ƙarƙashin ikon hukumomin tsaron tarayya, saboda haka gwamnatin jihar ba ta da hurumin tabbatarwa ko musanta rahotannin. Ya buƙaci manema labarai su tuntubi Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) da Hukumar Tsaro ta DSS domin samun cikakkun bayanai.

Haka kuma, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Bala Salisu Zango, ya ce bai da masaniya kan wani sammacin kame da aka yi wa waɗanda ake zargin.

Lamarin ya biyo bayan sanarwar Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, cewa an cafke wasu mutane bakwai da ake zargin suna da alaƙa da Boko Haram da ISWAP bayan dawowarsu daga aikin Hajji, yayin da gwamnatin Katsina ta ci gaba da musanta zarge-zargen cewa ta tallafa wa wasu ƴan bindiga zuwa aikin Hajji.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments