Ana binciken kyaftin ɗin tawagar ƙwallon ƙafa ta kasar Cape Verde, Ryan Mendes, kan zargin yi wa wata mata mai aikin fassara fyade yayin da tawagar ke kasar New Zealand domin buga wasan sada zumunta a watan Maris na 2026.
Matar ta yi zargin cewa Mendes ya shiga ɗakinta na otal ba tare da izini ba, inda ta ce ya kai mata hari tare da cin zarafinta. Ta kuma ce ta miƙa wa ‘yansanda hotunan raunukan da ta samu a jikinta a matsayin hujja.
Jami’an ‘yansandan New Zealand sun fara bincike kan lamarin, inda suka tattara shaidu daga kyamarorin tsaro na otal tare da jiran sakamakon binciken ƙwararru kafin yanke hukunci kan mataki na gaba.
Har zuwa yanzu, Ryan Mendes bai yi wata magana kan zarge-zargen ba, yayin da FIFA ta ce tana haɗin gwiwa da hukumomin New Zealand kuma tana ɗaukar lamarin da muhimmanci.