Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroYan bindiga sun kashe shugaban Miyetti Allah bayan halartar taron sulhu

Yan bindiga sun kashe shugaban Miyetti Allah bayan halartar taron sulhu

Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN) na jihar Benue, Ardo Muhammad, ya rasa ransa bayan wasu ’yan bindiga sun kai masa hari a ƙaramar hukumar Otukpo.

Rahotanni sun ce an kashe Ardo Muhammad tare da wani mutum mai suna Yakubu Isah a lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida, lamarin da ya jefa al’ummomin Otukpo da Ohinmini cikin fargaba.

An bayyana cewa kafin harin, marigayin ya halarci wani taron zaman lafiya da aka shirya tsakanin shugabannin al’ummar Ayunne da makiyaya a ƙaramar hukumar Ohinmini.

An ce taron na da nufin sasanta rikicin da ya daɗe yana addabar yankin.

Sai dai bayan kammala taron, wasu ’yan bindiga sun yi musu kwanton bauna a wani ƙauye da ke Otukpo, inda suka bude musu wuta tare da kashe su.

Ɗaya daga cikin ‘ya’yan marigayin ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an tare motar mahaifinsa kafin a kashe shi.

Shugaban ƙaramar hukumar Otukpo, Maxwell Ogiri, shi ma ya tabbatar da harin, yana mai cewa kisan ya haddasa tashin hankali a yankin.

Ya bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu, tare da tabbatar musu cewa jami’an tsaro sun fara bincike domin gano tare da cafke waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments