Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeMinistar Sweden ta halarci taron EU tare da jaririnta mai watanni uku

Ministar Sweden ta halarci taron EU tare da jaririnta mai watanni uku

Ministar Muhalli da Sauyin Yanayi ta ƙasar Sweden, Romina Pourmokhtari, ta halarci taron ministocin muhalli na Tarayyar Turai (EU) a ƙasar Luxembourg tare da jaririnta mai watanni uku, Adam, a wani mataki da ya ja hankalin jama’a.

Ministar Muhalli da Sauyin Yanayi ta ƙasar Sweden, Romina Pourmokhtari, ta halarci taron ministocin muhalli na Tarayyar Turai (EU) a ƙasar Luxembourg tare da jaririnta mai watanni uku, Adam, a wani mataki da ya ja hankalin jama’a.

Ministar mai shekara 30 ta ce hakan na nuna cewa mace na iya kasancewa uwa mai kula da ɗanta tare da ci gaba da gudanar da aikinta na gwamnati. Ta bayyana cewa ɗaya daga cikin abubuwan da ke sa Turai ta zama wuri mai kyau shi ne yadda ake ba mata damar haɗa aikin gwamnati da kula da iyali.

Wani jami’in Tarayyar Turai ya ce ana kyautata zaton wannan ne karo na farko da aka kawo jariri cikin irin wannan taron ministocin ƙungiyar.

Lamarin ya sake tayar da muhawara kan ƙalubalen da mata ke fuskanta wajen haɗa aikin yi da kula da yara. Bincike ya nuna cewa mata da yawa kan rasa damar ƙarin girma a aiki ko karin albashi bayan sun haihu.

A baya, tsohuwar Firaministar New Zealand, Jacinda Ardern, ta taɓa zuwa taron Majalisar Ɗinkin Duniya tare da jaririyarta a shekarar 2018, yayin da ’yar siyasar Australia Larissa Waters ta kafa tarihi a 2017 bayan ta shayar da jaririnta nono a zauren majalisar dokokin ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments