Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroKafa ‘yan sandan jihohi kaɗai ba zai magance rashin tsaro ba muddin...

Kafa ‘yan sandan jihohi kaɗai ba zai magance rashin tsaro ba muddin akwai talauci – Femi Falana

Fitaccen lauya mai rajin kare haƙƙin bil’adama, Femi Falana SAN, ya ce kafa rundunar ‘yan sandan jihohi ba zai kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a Najeriya ba, matuƙar ba a magance talauci da rashin aikin yi ba.

Falana ya bayyana haka a shirin Politics Today na Channels TV, inda ya ce gwamnati ta fi mayar da hankali kan sauya tsarin tsaro maimakon magance tushen matsalar da ke jefa matasa cikin aikata laifuka.

Ya kuma tunatar da cewa an taɓa amfani da tsarin ‘yan sandan yankuna a Jamhuriya ta Farko, amma daga baya aka soke shi saboda yadda wasu shugabanni suka riƙa amfani da rundunar wajen muzgunawa abokan hamayya.

A cewarsa, idan za a dawo da tsarin ‘yan sandan jihohi, dole ne a samar da isassun matakan kariya da za su hana cin zarafin iko, tare da la’akari da yadda wasu jihohi ke fama da matsalar biyan albashi da fansho.

Wannan na zuwa ne bayan Majalisar Dattawa ta amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da zai bai wa jihohi damar kafa rundunonin ‘yan sandansu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments