Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAna zargin bullar sabuwar ƙungiyar ta’addanci mai suna ‘Sai Malam’ a jihar...

Ana zargin bullar sabuwar ƙungiyar ta’addanci mai suna ‘Sai Malam’ a jihar Kebbi

Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana damuwarta kan bullar wata sabuwar ƙungiyar ta’addanci mai suna “Sai Malam”, tana mai kira ga jami’an tsaro su ɗauki matakin gaggawa kafin ƙungiyar ta samu gindin zama.

Mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin tsaro na cikin gida, Kanal Hassan Riba (mai ritaya), ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki da Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, wanda mataimakinsa DIG Sulaiman Abdul ya wakilta.

A cewarsa, an fara gano ƙungiyar ne a Masarautar Zuru, inda jami’an tsaro suka tarwatsa ta. Sai dai ya ce an sake gano mambobinta a yankin Argungu.

Riba ya yi zargin cewa mambobin ƙungiyar na amfani da jini wajen gudanar da wasu al’adu a tsakaninsu, tare da kira ga rundunar ’yan sanda da ta ɗauki matakin murƙushe su cikin gaggawa.

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar na ci gaba da bai wa jami’an tsaro tallafin kayan aiki da motocin sintiri domin ƙarfafa yaƙi da rashin tsaro, yayin da aka tura jami’an Mopol zuwa Ƙaramar Hukumar Danko-Wasagu domin dakile kutse na ’yan bindiga.

A nasa jawabin, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, ta bakin DIG Abdul, ya ce dole ne jami’an tsaro su fara tattara bayanai kan sabuwar ƙungiyar kafin ta samu ƙarfi. Ya kuma buƙaci ƙarin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya da al’ummomi domin yaƙi da miyagun laifuka.

DIG Abdul ya kuma roƙi jama’a da su rika bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen kare rayuka da dukiyoyi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments