Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroGwamnan Sokoto ya alakanta matsalolin tsaro da shen miyagun kwayoyi

Gwamnan Sokoto ya alakanta matsalolin tsaro da shen miyagun kwayoyi

Gwamnan Jihar Sokoto Ahmed Aliyu, ya bayyana cewa mafi yawan matsalolin tsaron da jihar ke fuskanta na da nasaba da shaye-shayen miyagun kwayoyi, yana mai cewa kusan kashi 80 cikin 100 na laifuffukan tashin hankali suna da alaka da shen miyagun kwayoyi.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wani taron da aka shirya domin tunawa da Ranar Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi ta 2026, inda mataimakinsa, Alhaji Idris Mohammed Gobir, ya wakilce shi.

Ya ce shaye-shayen miyagun kwayoyi na daga cikin manyan kalubalen da ke barazana ga makomar matasa da ci gaban al’umma, tare da jaddada cewa yana taimakawa wajen karuwar ayyukan ta’addanci, rusa iyalai, da kuma haddasa matsalolin lafiya da zamantakewa.

Gwamnan ya yi kira ga gwamnati, iyaye da sauran masu ruwa da tsaki da su hada kai domin dakile yaduwar shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments