Mutumin da ya fi kowa arziƙi a duniya, Elon Musk, ya yi barazanar ɗaukar matakin shari’a kan wasu ‘yan Majalisar Dokokin Amurka bayan sun zarge shi da cewa rage kasafin kuɗin gwamnatin Amurka ta hannun Ma’aikatar DOGE ya janyo mutuwar miliyoyin yara a Afirka.
Masu sukar matakin rage ko rufe wasu ayyukan Hukumar Tallafin Ƙasashen Waje ta Amurka (USAID) sun ce hakan ya shafi shirye-shiryen lafiya da agaji a ƙasashe masu tasowa.
Sai dai Musk ya musanta zargin, yana mai cewa ba zai zuba ido ana yaɗa irin waɗannan iƙirari ba, kuma zai nemi hakkinsa a kotu.