Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiYan Sandan Najeriya za ta fara saka kyamarori a jikin jami’anta yayin...

Yan Sandan Najeriya za ta fara saka kyamarori a jikin jami’anta yayin aiki

Rundunar ’yan sanda ta fara wani sabon shiri na zamanantar da ayyukan tsaro.

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya na shirin fara amfani da na’urorin daukar hoto da bidiyo da jami’anta za su rika sanyawa a jikinsu yayin gudanar da aiki, domin inganta gaskiya, riƙon amana da kuma ƙarfafa amincewar jama’a.

Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda mai kula da horaswa da ci gaban jami’ai, DIG Frank Mba, ya ce wannan mataki na daga cikin sauye-sauyen da rundunar ke aiwatarwa domin zamanantar da ayyukanta.

A cewarsa, amfani da na’urorin zai taimaka wajen rage zarge-zargen cin zarafi, tabbatar da adalci yayin gudanar da aiki, da kuma samar da sahihan hujjoji idan aka samu saɓani tsakanin jami’an tsaro da jama’a.

Ya ƙara da cewa ƙwarewa, gaskiya da mutunta haƙƙin jama’a su ne ginshiƙan nasarar aikin ’yan sanda a wannan zamani.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments