Dan takarar shugabancin Najeriya na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya bukaci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi murabus daga mukaminsa, yana mai danganta kiran da tabarbarewar tattalin arziki, matsalar tsaro da kuma abin da ya kira gazawar gwamnati wajen gudanar da mulki.
Obi ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya yi tsokaci kan sanarwar da Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya yi na shirinsa na yin murabus daga mukaminsa.
Ya ce murabus din Starmer ya nuna yadda shugabanni a kasashen da suka ci gaba ke daukar alhakin sakamakon gazawa wajen cika alkawuran da suka dauka ga al’umma.
A cewarsa, kafin zaben 2015, Tinubu ya kasance cikin masu kira ga tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan da ya sauka daga mulki sakamakon matsalolin tsaro da tattalin arziki, musamman bayan aukuwar sace daliban Chibok.
Obi ya tunatar da alkawuran da Tinubu ya yi a lokacin yakin neman zaben 2023, ciki har da inganta wutar lantarki, yaki da cin hanci da rashawa, inganta tsaro da kuma rage wahalhalun rayuwa.
Sai dai ya ce bayan kusan shekaru uku a mulki, yawancin alkawuran ba su cika ba, inda ya ce matsalar wutar lantarki, garkuwa da mutane da tsadar rayuwa sun ci gaba da ƙaruwa.
Ya kuma zargi cewa wasu fannoni kamar ababen more rayuwa, sufuri da yaki da rashawa sun kara tabarbarewa maimakon inganta.