Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAna zargin ’yan daba sun kashe budurwa yayin kwacen waya a Kano

Ana zargin ’yan daba sun kashe budurwa yayin kwacen waya a Kano

Rahotanni daga unguwar Hotoro da ke birnin Kano sun ce wata budurwa ta rasa ranta bayan wasu da ake zargin ’yan daba ne masu kwacen waya sun kai musu hari.

Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne lokacin da budurwar ta kai ziyara tare da saurayinta a unguwar, inda ake zargin yan daban sun tare su tare da kwace wayarta.

An ce harin ya yi sanadin mutuwar budurwar, yayin da saurayin nata ya samu munanan raunuka. Rahotanni sun nuna cewa ana zargin ya samu tabuwar kwakwalwa sakamakon harin, kuma an garzaya da shi zuwa asibiti domin kula da lafiyarsa.

Ya zuwa yanzu, jami’an tsaro ba su fitar da cikakken bayani kan lamarin ba, yayin da ake ci gaba da jiran karin bayani daga hukumomin da abin ya shafa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments