Sunday, October 18, 2026
HomeIlimiwani abu da ake zargin bom ne ya fashe a jihar Lagos

wani abu da ake zargin bom ne ya fashe a jihar Lagos

Kwamishinan ‘yan sandan Lagos, Fatai Tijani, ya tabbatar da cewa yankin kasuwar Mushin yana cikin aminci duk da fashewar abin da ake zargin bam ne a ƙarƙashin wata mota.

Kwamishinan ‘yan sandan Lagos, Fatai Tijani, ya tabbatar da cewa yankin kasuwar Mushin yana cikin aminci duk da fashewar abin da ake zargin bam ne a ƙarƙashin wata mota.

Ya ce jami’an EOD sun killace wurin nan take, suka gudanar da bincike kuma suka gano cewa mutum ɗaya ne ya samu rauni, wanda ke karɓar magani a asibiti.

Rahoton farko ya nuna an dasa bam ɗin ne a gefen fasinja na motar, kuma ya fashe lokacin da aka kunna injin ta.

Bayan bincike, ba a ƙara samun wani abu mai fashewa a yankin ba, yayin da aka tattara ragowar domin bincike na ƙwararru.

‘Yan sanda sun roƙi jama’a su kwantar da hankali su yi watsi da jita-jita, suna mai tabbatar da cewa Lagos na cikin tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments