Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga kamfanonin da ke samar da siminti a Najeriya da su saukaka farashin Siminti domin rage wa ’yan ƙasa radadin tsadar rayuwa da kuma bunƙasa ayyukan gine-gine a faɗin ƙasar.
Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ya bayyana hakan ne yayin bikin ƙaddamar da sabon sunan kamfanin Lafarge Africa, wanda yanzu zai ci gaba da aiki da sunan HBM, bayan da kamfanin HUAXIN Group na ƙasar Sin ya mallake shi.
Umahi ya jaddada cewa hauhawar farashin siminti na jefa ayyukan gine-ginen gwamnati cikin ƙalubale, saboda yana ƙara yawan kuɗaɗen aiwatar da kwangiloli tare da tilasta sake nazarin kasafin kuɗinsu.
Ya ƙara da cewa rage farashin siminti zai taimaka wajen bunƙasa ayyukan raya ƙasa da kuma sauƙaƙa wa jama’a damar gina gidaje da sauran muhimman gine-gine.