Kwamishinan ’yan sandan Jihar Rivers ya cire DPO na ofishin ‘yan sanda na Oyigbo daga mukaminsa bayan zargin cewa ya karɓi rashawar naira 500,000 tare da amfani da mukaminsa ba bisa ƙa’ida ba.
Rahotanni sun ce an ɗauki matakin ne bayan wani mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam ya yi zargin cewa jami’in ya karɓi kuɗin daga hannun wani da aka tsare a ofishin ’yan sanda, duk da cewa ba a bayyana wani laifi da ya aikata ba.
Ana sa ran hukumar ’yan sanda za ta gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin tare da ɗaukar matakin da ya dace.