Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiYan sanda sun cafke wandnda ake zargi da kashe malamar Islamiyya a...

Yan sanda sun cafke wandnda ake zargi da kashe malamar Islamiyya a Kaduna

Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da cewa wasu fusatattun mutane sun kashe wata malamar Islamiyya tare da kona gawarta a yankin Maraban Jos a ranar Lahadi, 21 ga Yuni, 2026.

A cewar kakakin rundunar, Mansur Hassan, lamarin ya faru ne bayan wasu mutane sun zargi matar da satar yara, duk da cewa babu wata hujja da ta tabbatar da zargin.

Ya bayyana cewa da misalin karfe 10:00 na safe ne jami’in kula da ofishin ‘yan sandan Maraban Jos ya samu kiran gaggawa game da harin.

Daga nan jami’an ’yan sanda suka isa wurin, suka ceto matar tare da kai ta ofishin ’yan sanda domin ba ta kariya yayin da ake gudanar da bincike.

Sai dai daga baya, wani taron mutane masu yawa ya mamaye ofishin ‘yan sandan, inda suka rinjayi jami’an da ke bakin aiki, suka fitar da matar daga tsare, suka kashe ta sannan suka kona gawarta.

Rundunar ta bayyana lamarin a matsayin dabbanci da kuma daukar doka a hannu, tana mai jaddada cewa babu wani mutum ko rukuni da ke da ikon hukunta wani ba tare da bin doka ba.

’Yan sandan sun ce an kama wasu da ake zargi da hannu a wannan aika-aika, yayin da ake ci gaba da neman sauran wadanda suka tsere.

Sun kuma tabbatar da cewa ana gudanar da cikakken bincike domin gurfanar da duk masu hannu a gaban kotu.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kaduna, Rabiu Muhammad, ya gargadi jama’a da su guji daukar doka a hannunsu, yana mai kira da a rika kai rahoton duk wani abin da ake zargi ga jami’an tsaro domin su dauki matakin da ya dace bisa doka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments