Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiBello Turji ya yi ikirarin kashe sojoji a jihar Sokoto

Bello Turji ya yi ikirarin kashe sojoji a jihar Sokoto

A cikin bidiyon, Turji ya ce mayaƙansa sun yi artabu da dakarun soji, inda ya yi iƙirarin cewa sun kashe wasu daga cikinsu tare da ƙwato dabbobin da ya ce jami’an tsaro sun karɓe musu. Haka kuma, ya yi barazanar ci gaba da kai hare-hare idan ba a daina farmakarsu ba.

Rahotanni sun ce kalaman nasa na zuwa ne bayan wani hari da aka kai kan sojoji a ƙaramar hukumar Isa ta Jihar Sokoto, inda fashewar wani bam da ake zargin ’yan bindiga ne suka dasa ya yi sanadin mutuwar wasu sojoji tare da jikkata wasu.

Sai dai hukumomin tsaro ba su tabbatar da ikirarin da Turji ya yi a cikin bidiyon ba, kuma ba su fitar da wata sanarwa kan sabon faifan bidiyon ba har zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments