Dandalin Masu Ruwa da Tsaki na Jam’iyyar PRP a shiyyar Arewa maso Yamma ya zargi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da yunƙurin mallake tikitin takarar jam’iyyun siyasa ta hanyar sayen fom ɗin takara, tare da barazanar maka shi a kotu.
Shugaban dandalin, Abdullahi Musa Giza, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Kano. Ya ce an saye fom ɗin takara na dukkan muƙamai 69 na jam’iyyar PRP ta hannun mutum guda da ba mamba ba ne, lamarin da ya ce na iya hana mambobin da suka cancanta damar neman tikitin takara.
Giza ya kuma yi zargin cewa irin wannan mataki ya faru a wasu jam’iyyu fiye da bakwai, inda ya ce ana danganta Kwankwaso da shirin. A cewarsa, hakan na barazana ga dimokuraɗiyya da tsarin gudanar da harkokin cikin gida na jam’iyyun siyasa.
Ya jaddada cewa PRP ba za ta amince da duk wani yunƙuri na katsalandan cikin harkokinta ba, tare da kira ga Kwankwaso da ya mutunta ‘yancin jam’iyyun siyasa. Ya kuma yi gargaɗin cewa idan aka ci gaba da abin da suka kira tsoma baki, za su garzaya kotu domin kare haƙƙin mambobinsu da martabar jam’iyyar.